Isa ga babban shafi
Tunisia - Siyasa

Shugaban Tunisia ya dakatar da majalisar dokoki har sai abinda hali yayi

Shugaban kasar Tunisia Kais Sa’ed ya bayyana tsawaita dokar dakatar da ‘yan majalisun kasar har illa masha Allahu.

Shugaban kasar Tunisia Kaïs Saïed.
Shugaban kasar Tunisia Kaïs Saïed. REUTERS - Zoubeir Souissi
Talla

Shugaba Sa’ed ya dauki wannan matakin ne wata guda bayan dakatar da su da kuma baiwa kansa karin karfin fada aji.

A jawabin da ya yiwa al’ummar kasar, shugaban ya bayyana majalisar dokoki da jam’iyyun siyasar kasar a matsayin masu hatsari ga al’ummar sa.

Tuni dai wannan mataki na shugaban Tunusia ya gamu da mummunar suka daga ‘yan siyasa da kuma masu kare hakkin dan Adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.