Isa ga babban shafi
Tunisia-Siyasa

Kuri'ar jin ra'ayin jama'ar Tunisia ta amince da tsarin shugaba mai cikakken iko

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da shugaban kasar Tunisia Kais Saied ya gabatar ta yanar gizo da ba ta samu halartar masu zabe dayawa ba, ta amince da tsarin mulkin shugaban kasa mai cikakken iko, bisa tsarin da kasar ke bi yanzu na gamin gambiza, kamar yadda sakamakon hukumar ya nunar.

Shugaba Kais Saied na Tunisia.
Shugaba Kais Saied na Tunisia. AFP - FETHI BELAID
Talla

Sakamakon wannan kuri’a ta jin ra’ayin 'yan kasa da aka gudanar a tsakanin ranakun15 ga watan janairu zuwa 20 ga watan Maris da ya gabata da aka gabatarwa shugaba Saied a jiya alhamis a lokacin wani taro da ya samu halartar Firaminista Najla Bouden da ministan fasaha, Nizar Ben Néji, kamar yadda hoton Bidiyon da aka yada a yau juma’a ya nunar.

Gudanar da wannan zaben raba gardama ta yanar gizo na tafiya ne a karkashin manufofin da shugaba Kais Said ya gabatar a watan disamban bara domin kawo karshen rikicin siyasar kasar bayan da ya samu cikakke iko a watan yuli ta hanyar rusa gwamnati tare da dakatar da aikin majalisar dokoki wadda daga karshe a larabar makon nan ya kammala rusawa.

Firaminista Ben Néji ya bayyana cewa mutane dubu 534 da 915 ne suka halarci kada kuri’ar ta yanar gizo, da ke bude ga ko wane dan kasar Tunisa da ke da sama da shekarun haihuwa 16.

Kasar Tunisia nada kimanin mutane miliyan 12, a lokacin zaben da ya gabata na 2019 hukumar zaben kasar ta bayyana cewa kimanin yan kasar da ke da shekaru sama da 18 su kimanin miliyan 7 da dubu dari 7 ne suka halarci zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.