Isa ga babban shafi
Tunisia-Shari'a

Sabuwar Majalisar shari'ar Tunisia ta sha rantsuwar kama aiki

Mambobin hukumar wucin gadi da ke kula da zura ido kan harakokin shara’a a kasar Tunisia, sun karbi rantsuwar soma aiki, don maye gurbin hukumar kolin alkalan kotun shari'ar kasar CSM wace rusa ta da shugaba Kais Sa'ied ya yi, ya Haifar  da gagarumar suka a ciki da wajen kasar ta Tunisia.

Ginin Majalisar Shari'ar Tunisia.
Ginin Majalisar Shari'ar Tunisia. REUTERS - ZOUBEIR SOUISSI
Talla

A lokacin bikin kaddamar da hukumar a fadar shugaban kasa, gaban mamabobin sabuwar hukumar kolin shara’ar ta wucin gadi da ya nada, shugaba  Kais Saied, ya bayyana lokaci da zama  mai cike da tarihi, da ya tabbatar da yancin fannin shara’ar gaskiya a kasar.

Bayan da ya dakatar da aikin majalisar dokoki, tare rusa gwamnati a watan yunin bara, haka kuma a ranar 5 ga watan fabrairun da ya gabata ne shagaba Sa'ied ya rusa hukumar kolin mai kula da harakokin shara’ar kasar CSM, hukuma mai zaman kanta da aka kirkiro a 2016 domin nada alkalan shara’a a kasar.

M. Saied, na kakkausan suka kan alkalan ne da yake zargi da zama yan rashawa, ya kuma zargi hukumar ta CSM da jan kafa wajen gudanar da bincike kan kisan da aka aikata a 2013 kan wasu masu sassaucin ra’ayi 2, Chokri Belaid da Mohamed Brahmi.

Har ila yau ya zargin CSM da zama wace jam’iyar da ke da ra’ayin musulunci ta Ennahdha ke juyawa yadda taga dama.

Kudirin fadar shugabancin kasar da ya samar da wannan sabuwar hukuma ne, ya bai wa shugaban kasar karfin ikon tsige duk wani alkali da ya kasa sauke nauyin aikin da ya rataya a wuyansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.