Isa ga babban shafi

Shugaban Tunisia ya rusa majalisar dokokin kasar

Shugaban Tunisia Kais Sa’id ya rusa majalisar dokokin kasar wadda ya dakatar da ayyukanta kimanin watanni 8 da suka gabata, matakin da ke ya kara jefa kasar a cikin wadi na rikicin siyasa.

Shugaban Tunisia Kaïs Saïed
Shugaban Tunisia Kaïs Saïed AFP - KARIM JAAFAR
Talla

Shugaba Kais ya sanar da rusa majalisar ne a jawabin da ya gabatar cikin daren jiya, sa’o’i kadan bayan da aka ruwaito cewa ‘yan majalisar sun gudanar da zama ta hoton bidiyo.

Yayin ganawar da suka yi, ‘yan majalisar sanar da cewa sun dawo bakin aiki tare da soke illahirin dokoki na musamman da shugaban ya kafa a watanni 8 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.