Isa ga babban shafi
TUNISIA

Shugaban Tunisiya ya rusa majalisar koli ta shari'a bisa zargin nuna son kai

Shugaban kasar Tunisiya Kais Saied ya rusa wata Majalisar koli mai zaman kanta da ke sa ido kan shari'a a kasar, yana zarginta da nuna son kai, a wani mataki na baya bayan nan da ya janyo cece-kuce tun bayan korar gwamnatin kasar a bara.

Shugaban kasar Tunisia Kais Saied, 2/9/2020.
Shugaban kasar Tunisia Kais Saied, 2/9/2020. Fethi Belaid AFP/File
Talla

Tun a ranar 25 ga watan Yulin da ya gabata, Saied ya kara karfin ikonsa, lokacin da ya kori gwamnati tare da narke majalisar dokokin kasar.

'Yan Tunisiya da dama sun yi maraba da matakin da ya dauka na adawa da tsarin siyasar da aka kwatanta da na cin hanci da rashawa da kuma rashin karsashi.

Amma jiga-jigan ‘yan siyasa da kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi gargadin na iya zama mulkin kama karya, matakin da shugabannin duniya suka nuna matukar damuwa.

A wani mataki da ake sa ran zai kara haifar da tashin hankali, Saied da sanyin safiyar Lahadi ya sanar da rusa majalisar koli ta shari'a (CSM) yayin wata ganawa da ministocin gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.