Isa ga babban shafi
Tunisia - Coronavirus

Dokar Tilastawa mutane nuna shaidar rigakafin Korona ta soma aiki a Tunisia

Gwamnatin Tunisia ta ce daga yanzu ya zama dole dukkanin ‘yan kasar da kuma baki su nuna shaidar karbar allurar rigakafin cutar COVID-19 kafin samun damar shiga wuraren tarukan jama’a.

Wani mutum yayin karɓar allurar rigakafin cutar coronavirus a Tunis babban birnin kasar Tunisia. Hoton da aka dauka ranar 26 ga Afrilu, 2021.
Wani mutum yayin karɓar allurar rigakafin cutar coronavirus a Tunis babban birnin kasar Tunisia. Hoton da aka dauka ranar 26 ga Afrilu, 2021. © REUTERS/Jihed Abidellaoui
Talla

Karkashin dokar da shugaba Kais Saed ya sanar a Juma’ar da ta gabata, ana bukatar manyan jami'ai da sauran ma’aikata su nuna katin dake tabbatar da sun yi allurar rigakafin cutar Korona don samun damar gudanar da ayyukansu a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu.

Har ila yau, za a bukaci shaidar rigakafin kafin shiga gidajen abinci, otal-otal da wuraren yawon shakatawa.

Sabuwar ta Tunisia ta kuma nuna cewar za a dakatar da ma’aikatan da ba su yi allurar rigakafi ba a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu, har sai sun gabatar da shaidar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.