Al'ummar Tunisia sun koma karkashin dokar kulle saboda Korona
Gwamnatin Tunusia ta kafa dokar takaita zirga-zirgar jama’a a daukacin kasar da ta ce ta soma aiki daga yau Lahadi har tsawon mako 1, domin dakile yaduwar annobar Korona.
Wallafawa ranar:
Yayin sanar da matakin, Fira Ministan Tunisia Hichem Mechichi ya ce kafa dokar kullen ta wucin gadi ya zama dole, ganin yadda annobar ke barazanar durkusar da asibitoci da sauran cibiyoyin kula da lafiyar kasar, a daidai lokacin da cutar ke lakume rayukan akalla mutane 100 a kowace rana.
Fira Ministan ya kara da cewar yanzu haka Tunusia na fuskantar kalubale mafi muni a fannin kula da lafiyar ‘yan kasar.
A karkashin sabuwar dokar kulle ta Tunusia, Masallatai, manyan kasuwanni da za su kasance a rufe tsawon makon guda, zalika an haramta tafiye-tafiye tsakanin yankuna, an hana taruka da sauran nau’kan bukukuwa, sai kuma haramta fitar da aka yi tsakanin karfe 7 na dare zuwa 5 na safe.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu