Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta kwaso 'yan kasar ta 64 da ke makale a Tunisia

Gwamnatin Burkina Faso ta tura jirgin da ya kwaso ‘yan kasar ta da ke makale a Tunisia, sabida hare-haren nuna kyamar launin fata da su ke fuskanta.

Wasu daga cikin bakin hauren kasashen Afrika.
Wasu daga cikin bakin hauren kasashen Afrika. © Fethi Belaid - AFP
Talla

An samu ballewar rikici a Tunisia ne bayan kalaman nuna kyama da shugaban kasar Kais Saied ya yi kan ‘yan ciranin da ke kasar a watan da ya gabata.

A larabar da ta gabata, ‘yan uwan da abokan arziki da kuma jami’an gwamnatin Burkina Faso ne su ka tarbi ‘yan ciranin su 64 a babban birnin kasar Ouagadougou.

Ministan gwamnatin kasar Karamoko Jean Marie Traore ya ce hakkin gwamnatin su ne kare lafiya da kuma walwalar al’ummar kasar a duk inda su ke.

A zantawar da aka yi da daya daga cikin ‘yan ciranin Inoussa Guiebre da ya kwashe watanni 17 a Tunisia ya na gudanar da kananan sana’oi, ya ce sun sha wuya zaman da su ka yi a kasar.

Ya ce an kore su daga gidajen su, lamarin da ya sanya mutane kwashe kwanaki 17 a ofishin jakadancin Burkina Faso kafin kwaso su da aka yi.

Tun bayan kalaman na shugaba Saied, akwai kasashen yammacin Afrika irin su Guinea da Mali da kuma Ivory Coast da su ka tura jirage don kwaso ‘yan kasar su da ke Tunisia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.