Isa ga babban shafi

Masu fafutuka na zargin shugaban Tunisia da nuna wa bakin haure wariyar launi

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun zargi shugaban Tunisia Kais Sa’id da nuna wariyar launi da kuma furta kalaman nuna kiyayya, bayan da ya sha alwashin amfani da karfi wajen dakile kwararar bakin haure cikin kasarsa daga yankin kudu da saharar Afirka.

Wani mutum daga cikin bakin haure fiye da 50 suka yi  yunkurin tsallaka tekun Meditaraniya zuwa Turai daga Tunisia.
Wani mutum daga cikin bakin haure fiye da 50 suka yi yunkurin tsallaka tekun Meditaraniya zuwa Turai daga Tunisia. © Petros Karadjias/AP
Talla

Shugaban na Tunisia ya bayyana kwararar bakin hauren a matsayin shiryayyen tuggun makiya domin sauya tsarin zamantakewar al’ummar kasarsa, la’akari da  yadda bakin hauren ke haifar da tashe-tashen hankula, baya ga aikata sauran muggan laifuka.

Sai dai a martanin da ya maida, Ramadan Bem Amor kakakin kungiyar da ke rajin kare hakkin dan Adam ta Tunisia, ya zargi shugaba Kais da kwaikwayon matakan da wasu kasashen Turai ke dauka wajen murkushe kwararar bakin haure.

Ben Amor ya kuma caccaki shugaban na Tunisia da kokarin kawar da hankalin ‘yan kasar daga matsalolin da suke damunsu ta hanyar kirkirar makiyan da babu su.

Masu fafutukar kare hakkin dan Adam dai na kallon kalaman Kais Sa’id a matsayin alamar da ke nuna ya ba da kai bori ya hau, dangane da matsalin lambar da yake sha daga kasar Italiya, da ke neman hadin kansa don dakile bakin hauren da ke kwarara zuwa tsibirinsu na Lampedusa mai nisan kilomita 150 daga Tunisia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.