Isa ga babban shafi

Mutane 70 sun bace bayan nutsewar kwale-kwale a tekun Tunisia

Sama da mutane 70 ne suka bace a tekun Mediterrenean bayan da wani kwale-kwale da ke dauke da bakin haure da ya taso daga Libya ya nutse a makwabciyar kasar Tunisia.

Wani jirgin ruwan Birtaniya da ya ceto bakin haure a gabar tekun kasar 02/05/22.
Wani jirgin ruwan Birtaniya da ya ceto bakin haure a gabar tekun kasar 02/05/22. AP - Gareth Fuller
Talla

Kakakin hukumar tsaron Tunisiya Houcem Eddine Jebabli, yace Kwale-kwalen wanda ke dauke da mutane kusan 100 lokacin da ya nutse a tekun, ya kife ne a tashar ruwa ta Sfax ta kasar Tunisiya, inda jami'an tsaron gabar teku da sojojin ruwa suka yi nasarar ceto mutane 24 daga cikin ruwan.

Kasar Libya ta zama wata babbar tashar da bakin haure da ke neman isa Turai, wanda ta zama hanya mafi muni a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.