Isa ga babban shafi

'Yan ci rani fiye da dubu 3 sun mutu a teku yayin kokarin isa Turai a 2021

Majalisar dinkin duniya ta ce mutane fiye da dubu 3 ne suka mutu yayin tsallaka Tekun Mediterranean da kuma Atlantic a shekarar da ta gabata, a kokarinsu na ketarawa zuwa Turai, adadin ya ninka wanda aka samu a shekarar 2020.

Membobin kungiyar agaji ta Jamus mai suna Sea-Watch 3 yayin taimakawa bakin haure wadanda ke kan wani jirgin ruwan katako a tekun Bahar Rum, Fabrairu 26, 2021.
Membobin kungiyar agaji ta Jamus mai suna Sea-Watch 3 yayin taimakawa bakin haure wadanda ke kan wani jirgin ruwan katako a tekun Bahar Rum, Fabrairu 26, 2021. via REUTERS - Selene Magnolia/Sea-Watch
Talla

A cikin sabon rahoton da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta bukaci a gaggauta toshe dukkanin hanyoyin da ake samun mace-macen ‘yan gudun hijira da masu neman mafaka da kuma ‘yan cirani da ke kokarin isa Turai.

Rahoton ya ce, a shekarar da ta gabata, masu tsallakawa Turai ta tekun Mediterranean da kuma Atlantic dubu 3 da 77 ne suka mutu yayin da a shekarar 2020 mutane dubu 1 da 544 suka mutu.

Kakakin hukumar kula da masu gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Shabia Mantoo ya ce a farkon shekarar nan an samu karin mutane dari 478 wadanda suka mutu ko kuma suka bace bat.

Hukumar ta ce, a shekarar da ta gabata ‘yan cirani dubu 53 da dari 323 ne suka isa Italiya ta kwale-kwale wanda ya nuna an samu karuwar kashi 83 na wanda aka samu a shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.