Isa ga babban shafi

Bakin haure 14 ne suka nitse a gabar ruwan Tunisia

Masu gadin gabar ruwan Sfax dake kasar Tunisia sun ce baki 14 da suka fito daga yankin Afirka dake kudu da sahara ne suka nitse a ruwa sakamakon wani hadarin da aka samu daren jiya Laraba. 

Wasu daga cikin bakin haure da ke neman zuwa Turai ta tekun Libya
Wasu daga cikin bakin haure da ke neman zuwa Turai ta tekun Libya REUTERS
Talla

Sanarwar da jami’an suka gabatar tace an ceto baki 54 daga cikin wadanda suka tsira sakamakon kifewar da kwale kwalensu yayi, tare da tsamo gawarwaki 14 na wadanda suka mutu. 

Wannan hadari na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Tunisia Kais Saied ya kitsa kyamar baki bakaken fata dake zama a cikin kasar sa, bayan ya zarge su da aikata laifuffuka da kuma yunkurin sauya fasalin jama’ar kasar. 

Wannan matsalar ta haifar da musgunawa daruruwan bakin dake zama a kasar saboda yadda aka koresu daga gidajen haya, abinda ya sa daruruwa daga cikinsu suka fara barin kasar suna komawa kasashensu na assali. 

Alkaluma sun nuna cewar akwai baki sama da dubu 21 wadanda suke zama a Tunisia ba tare da takardu ba, kuma akasarinsu sun fito ne daga kasashen Afirka. 

Hukumomin kasar Italia sun ce akalla baki dubu 32 suka tsere daga Tunisia zuwa kasar kuma cikinsu harda ‘yan assalin Tunisian dubu 18, yayin da wasu dubbai suka gudu zuwa Libya mai fama da tashin hankali. 

Kasashen Afirka na bayyana shugaba Saied a matsayin mai nuna wariyar jinsi, amma kuma yayin ganawa da shugaban kungiyar ECOWAS Umaro Sissico Embalo shugaban na Tunisia ya bayyana kansa a matsayin cikakken ‘dan Afirka. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.