Isa ga babban shafi

Daruruwan bakin-haure sun tsere daga Tunisia bayan umurnin korar su

Wasu bakin haure 300 daga kasashen yammacin Afrika sun shirya tsaf don barin Tunisia a Asabar din nan bias fargabar jerin tashe tashen hankula da ya kunno kai tun bayan da shugaba Kais Saied ya bada umurnin yin dirar mikiya a kansu a watan da ya gabata.

Wasu bakin -haure da ke jiran tsammaani a ofishin jakadancin Ivory Coast bayan umurnin shugaba Saied. 24 ga Fabrairu, 2023.
Wasu bakin -haure da ke jiran tsammaani a ofishin jakadancin Ivory Coast bayan umurnin shugaba Saied. 24 ga Fabrairu, 2023. AFP - FETHI BELAID
Talla

A jawabin da ya gabatar a  ranar 21 ga watan Fabrairu, Saied ya umurci jami’an gwamnatinsa su dauki matakan gaggawa a kan  bakin hauren da ke shigowa kasar ba bisa ka’ida ba, inda ya  yi ikirari ba tare da wata shaida ba cewa akwai wani shiri da suke yi na aikata abin da ya kira  mugun laifi.

Saied ya yi zargin cewa bakin haure ne ke aikata akasarin manyan laifukan da ake yi a kasar da ke arewacin  Afrika, wadanda suka hada da tada garuruwa da kuma hare hare a kan kauyuka.

Kungiyar Tarayyar Afrika ta bayyana matukar kaduwa da damuwa  game da sahihancin kalaman Saied, a yayin da gwamnatocin kasashen Afrika ke fadi tashin shirya kwasar ‘yan kasashensu da  suka shiga ofisoshin jakadancinsu a firgice don neman taimako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.