Isa ga babban shafi

Tunisia ta sallami babbar jami'ar kungiyar kwadago ta Turai daga kasar

Shugaban Tunisiya Kais Saied ya ba da umarnin korar babbar jami'ar kungiyar kwadago ta turai a ranar Asabar din da ta gabata saboda wani jawabi da ta yi wanda aka kwatanta a "matsayin katsalandan ga harkokin cikin gidan kasar.

Shugaban Tunisa Kais Said
Shugaban Tunisa Kais Said AP - Slim Abid
Talla

A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce, bisa umarnin shugaba Kais Saied, hukumomin Tunisiya sun ba da umarnin ficewar Esther Lynch daga kasar ba tare da bata lokaci ba.

Sanarwar Ofishin shugaban kasar ta kara da cewa barinta tamkar barin barzana ga kasar ne, don haka ya zamar mata dole ta tattara yanata-yanata ta bar kasar.

Da safiyar yau ne Lynch ta yiwa dubban al’ummar kasar jawabin da ya kunshi adawar ta ga kamen manyan ‘yan adawar kasar da kuma yadda gwamnatin Kais Sa’eed ta gaza yin komai game da tabarbarewar tattalin arzikin kasar.

Lynch ta kuma kara da cewa tana goyon bayan masu zanga-zangar adawa da gwamnatin kasar su sama da miliyan 45, yayin da ta ce tana kira ga gwamnati da ta gaggauta sakin ‘yan adawa da wasu manyan ‘yan kasuwa da ta kama, yayin da ta ce kamata ya yi a zauna teburin sulhu da su a maimakon kamasu da kuma yi musu barzana.

Wannan dalili ya sa gwamnatin kasar ke ganin Lynch na yiwa zaman lafiyar kasar zagon kasa don haka ta dauki matakin sallamar ta

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.