Isa ga babban shafi

Masu zanga-zanga a Tunisia sun bukaci shugaban kasar ya yi murabus

Al’ummar Tunisia na wata gaggarumar zanga-zangar kira ga shugaban kasar Kais Sa’eed ya sauka daga kan mukaminsa, abin da ke zuwa a ranar tunawa da mutuwar tsohon shugaban kasar Ben Ali. 

Wasu masu zanga zanga a Tunisa.
Wasu masu zanga zanga a Tunisa. REUTERS - ZOUBEIR SOUISSI
Talla

Jama’ar Tunisia dai na nuna takaicin su game da halin kunci da bakin Talauci da suke zargin gwamnatin Kais Sa’eed ta jefa su ciki, sai kuma sake rarrabuwar kan siyasa da kasar ta sake fadawa. 

Jam’iyyar Ennahdha mai rajin kare manufofin addinin musulunci na cikin ‘yan gaba-gaba dake bukatar Sa’eed ya sauka daga mukamin sa ba tare da wani bata lokaci ba. 

Sa’eed wanda ya karbi mulkin kasar a watan Yulin 2021 na ci gaba da shan matsin lamba daga ciki da wajen kasar game da yadda yake da sha’awar zama shugaba daya Tilo dake da cikakken iko a kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.