Isa ga babban shafi

Al'ummar Tunisia na zaben 'yan majalisar dokoki a karkashin inuwar shugaba Saied

Al'ummar Tunisia sun kada kuri'a a yau asabar don sabunta majalisar dokokinsu, a kuri'ar da mafi yawan jam'iyyu suka kauracewa zaben, matakin karshe na gina tsarin nuna kishin kasa da shugaban kasar Kais Saied ya yi bayan juyin mulkin shekara daya da ta wuce.

Kayan zabe daga hukumar zaben Tunisia
Kayan zabe daga hukumar zaben Tunisia AFP - FETHI BELAID
Talla

Bayan kada kuri'a a Tunis da ke babban birnin kasar, shugaba Saied ya yi kira ga masu kada kuri'a miliyan 9 da su tashi tsaye. Ya na mai cewa "wannan dama ce ta tarihi don kwato muku haƙƙinku", "mun yi fatali da waɗanda suka lalata ƙasar", in ji shi.

'Yan kasar Tunisiya kadan ne suka gamsu a wasu ofisoshi da ke tsakiyar babban birnin kasar, wasu tsirarun masu kada kuri'a ne suka fito don kada kuri'ar.

Wasu daga cikin ma su zanga-zanga na kasar Tunisia
Wasu daga cikin ma su zanga-zanga na kasar Tunisia © Amira Souilem / RFI

Noureddine Jouini, shugaban ofishin, Rue de l'Inde, ya shaida wa AFP cewa "Mun san ba zai zama irin yadda aka saba yi ba, har ma ya yi kasa da yadda ake tsammani."

Sabanin wadannan binciken, shugaban hukumar zaben kasar Isie, Farouk Bouasker, ya tabbatar da cewa "har zuwa karfe 10:00 na safe, an sami kuri'u 270,032, adadi mai mahimmanci, idan aka kwatanta da kuri'ar raba gardama a lokacin rani da kuma zaben shugaban kasa na 2019".

Ali Béjaoui, wani lauya mai shekaru 48 da ya gana da shi a wani ofishi, rue de Marseille, ya shaida wa AFP cewa, "Zabuka wajibi ne kuma dole ne a yi shi." Bai taba faduwa zabe ba ko a karkashin mulkin kama-karya na hambararren shugaba Zine El Abidine Ben Ali.

Dole ne sabon zauren wakilai 161 ya maye gurbin wanda shugaba Saied ya rusa a ranar 25 ga yuli  na shekara ta 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.