Isa ga babban shafi

Tunisia za ta cire batun addini daga kundin mulkinta

Mutumin da shugaban kasar Tunisia Kais Saied ya nada domin rubuta wa kasar sabon kundin tsarin mulki ya sha alwashin gabatar da sabon kundin da ba zai ambaci addinin Islama ko da guda ba, saboda yaki da jam’iyyun da ke da nasaba da addinin.

Shugaban Tunisia Kais Saied
Shugaban Tunisia Kais Saied © AFP
Talla

Sharadi na farko na kundin tsarin mulkin kasar da aka amince da shi shekaru 3 da bayan juyin juya halin kasar da aka yi a shekarar 2011 ya bayyana cewar, kasar yar tanciya ce, mai cin gashin kanta, mai bin addinin Islama da kuma amfani da harshen larabaci.

Amma shugaban kwamitin rubuta kundin Sadeq Belaid yace kashi 80 na jama’ar kasar na kyamar tsatsauran ra’ayi da kuma kin amfani da addini domin biyan bukatar siyasa, saboda haka zasu share sharadin na farko.

Ana saran gabatar da sabon kundin ga shugaba Saied kafin ranar 25 ga watan gobe da za’a gudanar da zaben raba gardama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.