Isa ga babban shafi

Turkiya ta dage tattaunawa da kasashen Sweden da Finland kan shigarsu NATO

Turkiya ta dage tattaunawar shigar da kasashen Sweden da Finland cikin kungiyar tsaro ta NATO, lamarin da ya kara nuna rashin amincewa da fatan kasashen na shiga cikin kawancen tsaron kasashen yammacin duniya bayan da Rasha ta kaddamar da mamayar ta a Ukraine. 

Shugaba Recep Tayyib Erdogan.
Shugaba Recep Tayyib Erdogan. AP
Talla

Turkiya ta sanar da matakin ne kwana guda bayan da shugaba Recep Tayyip Erdogan ya caccaki kasar Sweden kan yadda ta kyale masu zanga-zanga a karshen mako suka kona kur’ani a kofar ofishin jakadancin ta da ke kasar. 

Wata majiyar diflomasiyya ta Turkiya ta ce an dage taron bangarorin uku ne daga watan Fabrairu zuwa wani lokaci na daban da ba’a sanar ba. 

Matakin dai ya kara rage damar da kasashen biyu ke da shi na shiga kungiyar tsaro ta NATO kafin lokacin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin Turkiya da za a yi a watan Mayu. 

Kasar Finland, wacce ke da iyaka da Rasha da kuma Sweden sun yanke shawara shiga kungiyar NATO ne inda kuma suka samu goyon bayan aniyar su a wani taron koli na kungiyar tsaro ta NATO da ya gudana a watan Yuni. 

Daga nan ne kasashe 28 daga cikin kasashe 30 na kungiyar tsaro ta NATO suka amince da bukatar kasashen biyu cikin gaggawa, toh amma dole ne sai dukkan mambobin kungiyar da Turkiya ke cikinta sun amince da bukatar shigar da su cikin kungiyar ta NATO. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.