Isa ga babban shafi

Da wuya a kawo karshen yakin Ukraine-Turkiya

Ministan tsaron Turkiya Hulusi Akar ya fada a yau asabar cewa yakin da ake yi a Ukraine da wuya a kawo karshensa cikin sauki.

Shugaban Turkiya  Recep Tayyip Erdogan,tare da rakiyar tawagar kungiyar tsaro ta Nato
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan,tare da rakiyar tawagar kungiyar tsaro ta Nato © Bernat Armangue/AP
Talla

Ministan ya kara sa da cewa "ba zai zama kuskure ba a ce duk da irin kokarin da kasashen Duniya ke yi na ganin an tsagaita bude wuta, akwai yiyuwar a ci gaba da yakin har zuwa shekara ta 2023" .

Turkiya na daga cikin kasashe memba a kungiyar tsaro ta NATO, ta kuma sanya kanta a matsayin  mai shiga tsakani a rikicin da ke tsakanin makwabtanta guda biyu da ke kan iyakar tekun Black Sea.

Turkiyya ta taimaka wajen cimma yarjejeniya da Majalisar Dinkin Duniya kan fitar da hatsin Ukraine daga tashoshin jiragen ruwa na Ukraine, tuni ta shirya wani taro tsakanin shugabannin diflomasiyyar Rasha da na Ukraine a farkon yakin a cikin watan Maris, da kuma gabatar da shawarwari tsakanin Rasha da Ukraine a Istanbul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.