Isa ga babban shafi

Zelensky ya isa Amurka don ganawa da Biden kan yakin Ukraine da Rasha

Shugaba Volodymyr Zelensky zai gana da Joe Biden na Amurka yau laraba a fadar White House yayin ziyarar da ya ke kaiwa Washington, ganawar da za ta mayar da hankali kan tallafin da kasar za ta baiwa Kiev a yakin da ta ke da Rasha.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky. AP - Efrem Lukatsky
Talla

Ziyarar wadda aka tsarata a asirce na zuwa ne a dai dai lokacin da shugaba Vladimir Putin na Rasha ke shirin ganawa da manyan hafsoshin Sojin kasar don jin bahasi kan nasarorin kasar a yakin da ta ke da Ukraine tare da tsara muradan da suke fatan cimmawa a shekara mai zuwa.

Kakakin fadar White House Karine Jean-Pierre cikin sanarwar da ta fitar game da ziyarar ta Zelensky ta ce yayin tattaunawar Amurka za ta sake jaddadawa Ukraine cikakken goyon baya a yakin da ta ke, haka zalika za ta aike da sako ga Rasha kan hadin kan kasashen yammaci.

Ziyarar dai ita ce irinta ta farko da Zelensky ke kaiwa wajen Ukraine tun bayan faro yakin kasar da Rasha a watan Fabarairu, inda ake sa ran ya gabatar da jawabi ga zaman majalisar kasar.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter Zelensky, tsohon dan wasan barkwanci da ya juye shugaban kasa, ya ce yana kan hanya don karfafa goyon bayan kasashen yammaci ga Kiev.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.