Isa ga babban shafi

Amurka ta gargadi China da Rasha kan nahiyar Afirka

Amurka ta yi gargadin cewa China da Rasha na tada zaune tsaye a Afirka tare da ci gaba da samun guraben zama a nahiyar, ta hanyar yiwa shugabannin Afirka alkawarin ba da tallafin biliyoyin daloli.

Shugaban China Xi Jinping kenan da takwaransa na Amurka Joe Biden,
Shugaban China Xi Jinping kenan da takwaransa na Amurka Joe Biden, AFP - SAUL LOEB
Talla

Shugabannin Afirka arba'in da tara ne suka halarci taron koli na farko na nahiyar da Amurka a cikin shekaru takwas, daidai lokacin da shugaba Joe Biden ke neman yin amfani da diflomasiyya don karfafa alaka da yankin.

Sakataren tsaro Lloyd Austin, a wani taro tare da shugabannin kasashen Afirka da dama a farkon taron na kwanaki uku, ya zargi abokan hamayyar Amurka da yin amfani da wata hanya ta daban wajen kulla hulda da kasashen nahiyar.

Austin ya ce, kasar China tana fadada sawun ta a Afirka a kowace rana ta hanyar karuwar tasirin tattalin arzikinta.

Biden na shirin zuba dala biliyan 55 ga Afirka cikin shekaru uku, Fadar White House ta ce Amurka za ta zuba jarin dala biliyan 4 nan da shekarar 2025 don horar da ma'aikatan kiwon lafiya na Afirka.

Taron ya kuma tattauna batun NASA, inda Najeriya da Ruwanda suka zama kasashen Afirka na farko da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar Artemis, wani shiri da Amurka ta jagoranta na neman hadin kan kasa da kasa kan balaguro zuwa duniyar wata, Mars da sauran su.

Yarjejeniyar Artemis, wadda tuni ta hada da kawayen Turai, da Japan da wasu manyan kasashen Latin Amurka, na zuwa ne a daidai lokacin da kasar China ke ci gaba da fadada shirinta na zuwa duniyar wata, yayin da takun-saka da Rasha ke barazana ga aikin da Amurka ke yi kan shirin sararin samaniya bayan yakin cacar baka.

Kasar China ta yi watsi da sukar da ake mata game da rawar da take takawa a nahiyar Afirka, inda jakadanta a birnin Washington, Qin Gang, ya ce bai kamata nahiyar ta zama wurin da ake yin gasar samun cimaka ga manyan manyan kasashen duniya ba.

Taron na Amurka da Afirka shi ne na farko tun bayan da Barack Obama ya gayyaci shugabanni a shekarar 2014, inda magajinsa Donald Trump ya kasance baya alaka sosai da nahiyar.

Har yanzu dai batun tsaro shi ne babban abin da Amurka ta mayar da hankali, inda ta yi amfani da taron wajen mayar da hankali kan wasu manyan matsalolin da nahiyar ke fama da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.