Isa ga babban shafi

Girgizar kasa mai karfin maki 6.1 ta afkawa wasu yankunan Turkiya

Girgizar kasa mai karfin maki 6.1 ta afkawa yankin arewa maso yammacin Turkiya da safiyar yau laraba inda bayanai ke cewa ta jikkata mutane 35.

Wani yanki na Turkiya da girgizar kasar ta afkawa.
Wani yanki na Turkiya da girgizar kasar ta afkawa. REUTERS - MURAD SEZER
Talla

Bayanai sun ce girgizar kasar ta yi mummunar barna a yankunan Duzce da Golyaka da ke da tazarar nisan kilomita 170 da birnin Istanbul, birni mafi girma a kasar ta Turkiya, inda yanzu haka hankula suka tashi.

Mahukuntan Turkiya sun ce karfin girgizar kasar ya zarta hasashen da Amurka ta yi na cewa za a samu girgizar kasa a yankin mai karfin maki 5.9, haka zalika hasashen ya sabawa yankunan da aka ga girgizar kasar a zahiri.

Dubban mutane ne yanzu haka aka kwashe daga yankunan na Duzce da Golyaka da Bolu da kuma Zonguldak wadanda ke cike da fargaba bayan faruwar girgizar kasar a safiyar yau.

Har yanzu dai babu rahoton rasa rai, sai dai tarin barna da kuma fargabar da girgizar kasar ta haifar a yankunan da ta afkawa.

Turkiya na sahun kasashen da ke yawan samun girgizar kasa lokaci zuwa lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.