Isa ga babban shafi

Girgizar kasa ta kashe akalla mutane 162 a kasar Indonesiya

Akalla mutane 162  ne suka mutu sakamakon wata girgizar kasa da ta afku a tsibirin Java na Indonesia a ranar Litinin.

Wani yanki da girgizar kasa ta shafa a kasar Indonesia
Wani yanki da girgizar kasa ta shafa a kasar Indonesia Antara Foto/Muhammad Adimaja/via REUTERS
Talla

Adam, kakakin karamar hukumar Cianjur a yammacin Java, wanda kamar yawancin 'yan Indonesiya ke da suna daya, ya shaida wa AFP cewa wannan adadi ne na wucin gadi ne saboda ba’a kai ga tantance adadin ba, inda gidaje da dama suka lalace.

Girgizar  kasa mai karfin maki 5.6 a ma’auninta ta afku ne a tsibirin Java na kasar Indonesia a ranar Litinin, inda ta kashe mutane da dama tare da lalata gine-gine da kuma haddasa zabtarewar kasa.

Babban jami’in da ke yankin yammacin Java da girgizar kasar ta fi kamari, ya ce an kidaya wadanda suka mutu a asibiti daya kadai, ba tare da bayar da takamaiman adadi ba, yayin da  wasu mutane da dam suka makale a wasu kauyuka da har yanzu ba a kai ga kwashe su ba.

Ya ce ‘yan uwan ​​wadanda lamarin ya rutsa da su sun taru a asibitin Sayang da ke garin, ya kuma yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa saboda har yanzu mazauna kauyukan da ke wajen garin na cikin makale.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.