Adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar Indonesia ya kai 252 a yanzu
Masu aikin ceto sun yi ta aikin lalubo wadanda suka saura da ransu a karkashin baraguzan gine gine a yayin da ‘yan uwa da abokai suka fara jana’izar masoyansu da suka mutu bayan girgizar kasar da ta lakume rayuka 252 a Tsibirin Java na kasar Indonesia.
Wallafawa ranar:
A yayin da ake ci gaba da zakulo matattu, hankali ya karkata ga wadanda ake tunanin suna da ransu, wadanda har yanzu ke karkashin baraguzai.
Inda wannan girgizar kasar da ta kai maki 5 da digo 6 ta fi yin tasiri shine garin Cianjur, indaa aaka fi samun akasarin wadanda suka mutu, kuma daruruwa suka jikkata a yayin da ake fargabar gwammai suna makale a cikin baraguzan gine ginen da da inda aka samu zaftarewar kasa.
A Talatar na ne adadin wadanda suka mutu a wannan iftila’in ya tashi zuwa 252 daga 162 tun da farko, kamar yadda wani kakakin gwamnati a. Cianjur ya baayyana.
A yau Talata shugaba Joko Widodo ya ziyarci yankin da lamarin ya auku, inda ya bada gudummawa ga wadanda abin ya shafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu