Isa ga babban shafi

Solomon Islands: Girgizar kasa mai karfin maki 7 ya razana mutane

Wata kakkarfar Girgizar kasa mai nauyin maki 7.0 ta afku a tsibirin Solomon Talatar nan, inda ganau suka ce sunji girgiza mai karfi tare da lalata turakun wutan lantarki a sassan babban birnin kasar Honiara.

Taswirar da ke nuna  Solomon islands, rda aka yi girgizar kasa.
Taswirar da ke nuna Solomon islands, rda aka yi girgizar kasa. AFP
Talla

Wani mai aiko wa AFP rahotanni a Honiara ya ce girgizar ta dauki kusan dakikoki 20.

Kawo yanzu dai babu wani rahoto da ke nuna barnar da aka samu a gine-ginen, amma wutar lantarki ta katse a wasu yankunan birnin kuma jama'a na ta tururuwa daga ofisoshinsu dake tsibiri suna guduwa zuwa tudu.

Rufin wani bangare na ofishin jakadancin Australia ya rufta, kamar yadda Fira minista Anthony Albanese ya shaida wa majalisar dokokin kasar, amma ya ce babu wanda ya samu rauni.

Gwamman ma’aikata sun arced aga ginin a lokacin da lamarin ya auku ddon guje wa jin rauni daga bbaraguzan da ke fadowa.

Ministan shari’ar kasar John Muria, ya wallafa hotuna a dandalin sadarwa na intanet.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.