Isa ga babban shafi

Girgizar kasa ta kashe mutane a Philippines

Akalla mutane biyar sun rasa rayukansu sakamakon wata girgizar kasa mai karfin maki 7 da ta auku a yankin arewacin Philippines a yau Laraba, yayin da kuma ta ruguza gine-gine da dama.

Wani gini da girgizar kasa ta lalata a Philippines
Wani gini da girgizar kasa ta lalata a Philippines AP
Talla

Girgizar kasar ta kuma wujijjiga dogayen gine-ginen da ke da tazarar kilomita 300 daga babban birnin kasar Manila, kuma ta auku ne da misalin karfe 8:43 na safiyar Larabar nan a lardin Abra da ke tsibirin Luzon.

An samu sama da mutane 100 da suka samu mabanbantan raunuka, inda kuma ibtila’in ya haddasa zabtarewar kasa da kuma katsewar wutar lantaki har ma da hanyoyin sadarwar intanet.

An dai ga yadda mutane suka yi ta kokarin ficewa daga gidajensu domin gudun fadowar buraguzai a kansu, sannan hatta manyan tituna sai da suka daddare kamar yadda wani hoton bidiyo da aka watsa a shafin Facebook ya nuna kuma kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya tabbatar da sahihancinsa.

Jami’an ‘yan sanda sun ce, yanzu haka akwai gidaje da dama da suka tsattsage, baya ga tagogionsu da suka tarwatse.

Kazalika wasu gine-gine masu dimbin tarihi da aka gina su tun lokacin da Spain ta yi wa kasar ta Philippines mulkin mallaka, su ma sun lalace a birnin Vigan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.