Isa ga babban shafi

Turkiya ta daure wani malami shekaru dubu 8 a gidan yari

Kotun birnin Santanbul na Turkiya ta yanke wa wani malami mai wa’azi a kafar talabijin hukunccin daurin shekaru dubu 8 da 658 a gidan yari bayan ta tuhume shi kan wasu laifuka.

Adnan Oktar (
Adnan Oktar ( DOGAN NEWS AGENCY/AFP/File
Talla

Malamin mai suna Adnan Oktar wanda ke da wani irin ra’ayi,  na yadda wata fahimtar addini da ke diga ayar tambaya game da asalin halittun duniya.

Malamin ya kan tara ‘yan mata masu nuna tsaraici domin kewaye shi a lokacin da yaake yin wa’azinsa.

A bara ne hukumomin Turkiya suka daure shi shekaru dubu 1 da 75 a gidan yari bisa samun sa da laifin cin zarafin mata da lalata kananan yara da damfara da kuma yunkurin yi wa sojojin kasar leken asiri.

Sai dai babbar kotun kasar ta janye wannan hukuncin na bara, amma a yanzu, wata kotun birnin Santanbul ta yanke masa daurin shekaru dubu 8 da 658 a gidan yari bayan ta tuhume shi da aikata laifuka da dama da suka hada da cin zarafin mata tare da take musu hakkokinsu kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar na Anadolu ya rawaito.

Malaman Musulunci na Turkiya sun sha caccakar malamin da suke yi masa kallon dan kungiyar asiri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.