Isa ga babban shafi

Kyandar biri ta kashe mutum na farko a Belgium

Ma’aikatar Lafiya a Belgium ta tabbatar da mutuwar mutum na farko sakamakon cutar kyandar biri ko kuma monkeypox wanda ke matsayin karo na 3 da aka samu irin wannan mutuwa tun bayan bullar cutar.

Wani mai fama da cutar kyandar biri a Turai.
Wani mai fama da cutar kyandar biri a Turai. AP - Francisco Seco
Talla

Turai da Amurka ne kan gaba da ke ganin masu kamuwa da wannan cuta ta kyandar biri inda zuwa yanzu su ke da jumullar masu dauke da cutar mutum dubu 50 da 496 ciki har da mutum 16 da suka mutu.

Tun cikin watan Yulin da ya gabata, hukumar lafiya ta Duniya WHO ta sanya cutar ta kyandar biri a sahun cutuka masu matukar hadari da ke bukatar daukar matakan gaggawa don dakile yaduwarta la’akari da ta ke da matukar barazana fiye da yadda ake tsammani.

WHO wadda ta sanya kyandar biri a sahun cutuka masu hadari irin Covid-19 da Ebola ta ce wajibi ne a mike tsaye don magance bazuwarta.

Belgium mai yawan jama’a miliyan 11 da rabi zuwa yanzu ta na da jumullar mutane 706 da suka harbu da kyandar biri ciki har da 32 da ke ciki mawuyacin hali, galibinsu masu auren jinsi.

Sanarwar da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar wadda ba ta bayyana sunan mutumin da cutar ta kashe ba, ta ce yau alhamis ne aka samu mara lafiya na farko da cutar ta kyandar biri ta kashe bayan shafe tsawon lokaci yana jinya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.