Isa ga babban shafi

NCDC ta sanar da karin masu kamuwa da kyandar biri a sassan Najeriya

Alkaluman hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Najeriya NCDC na nuna samun karuwar sabbin harbuwa da cutar kyandar biri a ilahirin jihohin kasar dai dai lokacin da duniya ke ci gaba da gargadi game da hadarin gaza daukar matakan yaki da cutar.

Ana ci gaba da samun karuwar sabbin kamuwa da cutar ta Monkeypox ko kuma kyandar biri ba kadai a Najeriya har da sauran sassan Duniya.
Ana ci gaba da samun karuwar sabbin kamuwa da cutar ta Monkeypox ko kuma kyandar biri ba kadai a Najeriya har da sauran sassan Duniya. AP
Talla

NCDC ta ce zuwa yanzu an samu karin adadin mutum 157 da aka tabbatar sun harbu da kyandar biri sai kuma wasu mutum 413 da ake kyautata zaton sun harbu da cutar duk da cewa har zuwa yanzu gwaji bai tabbatar ba.

Hukumar ta ce an samu bullar cutar ta kyandar biri a jihohin Najeriya 25 da kuma Abuja babban birnin kasar yayinda aka samu mace-macen masu dauke da cutar a jihohin Delta da Ondo da kuma jihar Akwa Ibom.

Alkaluman hukumar ta NCDC ta bayyana cewa akwai wasu da ake kyautata zaton sun harbu da wannan cuta da suka kunshi mutum 20 a jihar Lagos kana wasu 14 a jihar Ondo sai 13 a Adamawa sannan wasu mutum 12 a Delta kana wasu 12 a Bayelsa sai kuma mutum 11 a jihar Rivers.

Sauran jihohin da ke da mutanen da ake kyautata zaton sun harbu da cutar a baya-bayan nan akwai Edo mai mutum 8 kana Nasarawa mutum 8 da wasu mutum 6 a Anambra sai 5 a Abuja fadar gwamnatin kasar kana jihohin Taraba, Kwara da Kano da ke da mutum biyar biyar sannan mutum 4 a Imo wasu 3 a Cross River sai 3 a jihohin Borno da Cross River da Oyo da Abia da Gombe sannan mutum 2 a Katsina da Kogi kana mutum dai-dai a Niger da Ogun da Bauchi da da kuma Akwa Ibom.

A jumulla, NCDC ta ce zuwa yanzu Najeriya ta samu mutum 670 da suka harbu da cutar ta kyandar biri ko kuma Monkeypox.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.