Isa ga babban shafi

WHO ta sanar da fantsamar cutar kyandar biri zuwa kasashen Afrika 7

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce zuwa yanzu kusan mutum dubu 1 da 400 suka harbu da cutar kyandar biri a nahiyar Afrika bayan fantsamar cutar zuwa kasashe 7.

Cutar kyandar biri ta harbu mutane kusan dubu 4 a nahiyar Afrika.
Cutar kyandar biri ta harbu mutane kusan dubu 4 a nahiyar Afrika. AP
Talla

Shugabar hukumar ta WHO shiyyar Afrika, Matshidiso Moeti ta ce yanzu haka cutar ta kyandar biri ta bazu zuwa kasashen Kamaru da Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da kuma jamhuriyar demokradiyyar Congo kana Saliyo da Liberia da Najeriya da kuma Congo.

A cewar shugabar akwai mutane dubu 1 da 392 da ake kyautata zaton sun harbu da cutar cikin kasashen 7 ko da yak e zuwa yanzu mutum 44 kadai aka kai ga tabbatarwa.

Duk da cewa kasashen Afrika na ci gaba da ganin cutar a shekarun amma WHO ta ce yanayin yawan masu harbuwa da kuma saurin yaduwar cutar ya zarta yadda aka gani a 2021 lokacin da wasu kasashe suka samu bullar cutar.

Moeti ta yi gargadin barazanar nau’in cutar ta kyandar biri wadda ta ce ta sauya fasali kuma akwai banbanin yanayi tsakanin wadda ake gani a Afrika da kuma wadda ta bulla a Turai.

Hatta a Najeriya, har zuwa 2019 ana ganin bullar cutar ne kadai a kudancin kasar amma a baya-bayan nan ana samun bayanan bullarta a yankunan tsakiya gabashi da kuma arewacin kasar.

A cewar Matshidiso Moeti wajibi ne hada hannu don daukar matakin bai daya da nufin fatattakar cutar wadda aka fara ganin bullarta a ban kasa cikin shekarar 1970 a nahiyar inda ko a 2018 aka ga bullarta a kasashen Afrika 5 inda ta harbi miutane dubu 2 da 800.

A shekarar 2020 ma Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ta ga bullar cutar wadda ta harbi mutane dubu 6 da 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.