Isa ga babban shafi

An kaiwa cibiyoyin lafiya hare-hare sau 373 a kasashe 14 - WHO

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Gebreyesus ya bayyana matukar damuwa akan yadda ake kai hari kan asibitoci da kuma Cibiyoyin kula da lafiya musamman a kasashen da ake fama da tashin hankali.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus. AP - Salvatore Di Nolfi
Talla

Yayin da yake jawabin bude taron majalisar kula da lafiya ta duniya, Tedros ya ce a cikin wannan shekara kawai an kai irin wadannan hare hare har sau 373 a cibiyoyin kula da lafiya dake kasashe 14, inda aka kashe ma’aikata da marasa lafiya 154.

Tedros ya kuma ce su kansu jami’an Hukumar Lafiya basu tsira ba, ganin yadda aka kashe abokan aikin su Dakta Richard Muzoko daga Kamaru da Belinda Kasongo daga Congo wadanda aka hallaka su a Congo a shekarar 2019 lokacin da suke aikin kare mutane daga cutar Ebola.

Shugabannin Kasashen duniya tare da ministocin lafiya da kuma masana kula da harkokin lafiyar ne ke halartar taron Majalisar lafiya ta duniya karo na 75 a karkashin jagorancin Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.