Tedros Adhanom Gebreyesus zai sake jagorantar WHO a wa'adi na 2
Majalisar Lafiya ta Duniya ta sake zaben Tedros Adhanom Gebreyesus ‘dan kasar Habasha a matsayin wanda zai jagoranci Hukumar Lafiya ta Duniya na karin shekaru 5 masu zuwa ba tare da hamayya ba. Kasashen duniya 194 suka kada kuri’ar amincewa da shugabancin Tedros wanda ya fito daga kasar Habasha.
Wallafawa ranar:
Tuni Dr Tedros Adhanom Gebreyesus ya sha rantsuwar kama aiki a wa’adi na biyu na karin shekaru 5 a matsayin shugaban Hukumar Lafiya.
Tedros ya sha alwashin ci gaba da gudanar da aikin sa ba tare da tirsasawar wata kasa ko kuma wasu jama’a ba a matsayin sa na ma’aikacin duniya.
Shugaban ya yi amfani da damar wajen kira ga kasashen duniya da su mayar da zaman lafiya da fahimtar juna a matsayin maganin yaki.
Tedros mai shekaru 57 ya taba rike mukamin ministan lafiyar Habasha da kuma ma’aikatar harkokin waje, kafin nada shi a matsayin shugaban Hukumar Lafiyar ta Duniya WHO.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu