Isa ga babban shafi
HUKUMAR-LAFIYA

Tedros ya kama hanyar samun wa'adi na 2 a Hukumar Lafiya

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Gebreyesus ya kama hanyar ci gaba da jagorancin ta a wa’adi na biyu da zaran wa’adin sa ya kare saboda rashin samun abokin takarar jagorancin Hukumar.

Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Gebreyesus
Shugaban Hukumar Lafiya Tedros Gebreyesus AP - Denis Balibouse
Talla

Sanarwar da Hukumar ta gabatar yace bayan cikar wa’adin gabatar da ’Yan takarar jagorancin Hukumar ta Lafiya a ranar 23 ga watan Agustan wannan shekara, babu wani ‘dan takarar da ya gabatar da bukatar sa, sai Gebreyesus wanda kasashe 28 suka gabatar da sunan sa domin ci gaba da jagorancin Hukumar sakamakon rawar da ya taka wajen shawo kan matsalar annobar korona.

Daga cikin kasashen da suka goyi bayan shugaban domin ci gaba da jagorancin Hukumar akwai kasashen Turai 17 da suka hada da Austria da Faransa da Jamus da Netherlands da Portugal da Spain da Sweden da kuma ita kan ta kungiyar EU.

Alamar Hukumar Lafiya ta Duniya
Alamar Hukumar Lafiya ta Duniya Fabrice COFFRINI AFP/File

Kasashen Jamus da Spain sun ce goyan bayan Gebreyesus zai taimaka wajen shawo kan annobar korona ba tare da raba hankali ba, ganin yadda Hukumar ke bukatar jajircewa da jagoranci na gari irin na shi.

Daga cikin kasashen da suka goyi bayan takarar shugaban a wajen nahiyar Turai kuma akwai kasashen Bahrain da Barbados da Botswana da Tsibirin Cook da Indonesia da Kazakhstan da Kenya da Oman da Rwanda da Tonga da kuma Trinidad da Tobago.

Tedros mai shekaru 56 ya samu digirin sa na farko a bangaren kimiyar kwayar halitta a kasar sa ta Habasha, yayin da ya samu digiri na 2 da na 3 a bangaren kula da garkuwar jikin Bil Adama dake Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Birtaniya.

Alamar cutar korona
Alamar cutar korona via REUTERS - Social Media

Ya rike mukamin minista a Habasha kafin shekarar 2017 inda ya zama ‘dan Afirka na farko da ya samu damar jagorancin Hukumar Lafiya ta Duniya.

Gebreyesus ya fuskanci kalubale sosai daga shugaban Amurka na da Donald Trump sakamakon barkewar cutar korona, inda ya zarge shi da goyan bayan China wadda ake zargi da samar da cutar wadda ta lakume mutane sama da miliyan 5 ya zuwa wannan lokaci.

Wannan dalili ya sa Trump ya dakatar da kudaden da Amurka ke baiwa Hukumar da kuma janye kasar, kafin zuwan shugaba Joe Biden wanda ya dawo da kasar cikin ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.