Isa ga babban shafi

Cutar hanta na kashe mutane dubu 3 da 500 kowacce rana a sassan Duniya- WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce akalla mutane dubu 3 da 500 na mutuwa kowacce rana sakamakon ciwon hanta, cutar da ke ci gaba da ta’azzara a sassan Duniya, inda hukumar ta bukaci daukar matakai don dakile cutar wadda a yanzu ta koma ta biyu mafi saurin kisa a ban kasa.

Duk da raguwar sabbin masu kamuwa da cutar ta hanta, amma yanayin yadda cutar ke kisa na ci gaba da karuwa.
Duk da raguwar sabbin masu kamuwa da cutar ta hanta, amma yanayin yadda cutar ke kisa na ci gaba da karuwa. AFP
Talla

Wasu sabbin alkaluma da WHO ta tattara daga kasashe 187 ya nuna yadda adadin mutanen da ke mutuwa sanadiyyar cutar hanta duk shekara ya karu daga mutum miliyan 1 da dubu 1 a 2019 zuwa miliyan 1 da 300 a 2022.

A jawabinsa gaban zaman babban taron yaki da cutar ta hanta da ke gudana a Portugal, shugaban sashen yaki da cutar na WHO Meg Doherty ya shaidawa mahalarta taron cewa cikin mutanen dubu 3 da 500 da cutar ta hanta ke kashe kowacce rana kashi 83 sun yi fama da rukunin B sai kashi 17 masu rukunin C.

A cewar jami’in lura da wadattu da kuma arahar magunguna yaki da wannan cuta, sam bai kamata ta ci gaba da kasancewa barazana ga rayukan jama’a ba.

WHO ta bayyana cewa halin da ake ciki a yanzu ya sanya shakku kan yiwuwar iya cika muradin warkar da kashi 80 cikin dari na masu fama da cutar hantar kafin nan da shekarar 2030.

Yanzu haka dai akwai mutane akalla miliyan 12 da dubu 500 da suka warke daga cutar ta hanta, sai dai yanayin mutanen da cutar ke kashewa na karuwa duk kuwa da raguwa sabbin kamuwa da ita a sassan Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.