Isa ga babban shafi

An samu nasarar rage kaifin zazzabin cizon sauro a Ivory Coast

Bayanai daga Ivory Coast sun ce ma’aikatan kiwon lafiya na  samun gagarumar nasara, a kokarin da suke na dakile zazzaɓin cizon sauro a kasar, inda ya zuwa yanzu aka samu raguwar waɗanda ke kamuwa da cutar da sama da kashi 50 cikin 100.

yadda Cutar cizon sauro ke barna ga al'uma
yadda Cutar cizon sauro ke barna ga al'uma Rafael Neddermeyer
Talla

Jami’an kiwon lafiyar na Ivory Coast kimanin dubu 8 da 300 ne tare da tallafin kungiyar agaji ta ‘Save the Children’ suka duƙufa wajen wannan gagrumin aiki, inda suke amfani da kekuna wajen shiga ƙauyukan masu nisa da suka rasa hanyoyi, abinda ya ba su damar rage yawan masu kamuwa cutar zazzabin cizon sauron a wasu yankuna da aƙalla kashi 70 cikin 100 a shekarar bana.

Kasashen Afirka dake yankin kudu da Sahara ne ke kan gaba a duniya wajen fama da zazzabin cizon sauro, cutar da ke haddasa salwantar rayuka, akasari na ‘yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar da kwatankwacin kashi 80 cikin 100.

Wani  binciken masanan kuma ya sanya Ivory Coast cikin kashe 10 da suka fi fama da zazzabin cizon sauro, kasar da a cikin shekarar 2022 kaɗai ta ɗauki kaso 3 cikin 100 na ɗaukacin yawan waɗanda suka kamu da cutar a duniya.

A jiya Alhamis Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta jagoranci bikin zagayowar ranar yaƙi da zazzabin cizon sauro ta duniya, wadda ta yi amfani da ita wajen sabuntawa da kuma ƙarfafa matakan yaki da cutar, wadda ke laƙume rayukan yara kusan rabin miliyan a duk shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.