Isa ga babban shafi

An samu wani likita da safarar sassan jikin mutum a jihar Filato

Yanzu haka ana zaman dar dar a wasu sassan birnin Jos dake Jihar Filaton Najeriya, sakamakon yadda kotu ta bada belin wani likita da ake tuhuma da laifin sace sassan jikin marasa lafiya a asibitin sa. 

Kasar Masar ce kan gaba wajen safarar sassan jikin mutum, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
Kasar Masar ce kan gaba wajen safarar sassan jikin mutum, a cewar Majalisar Dinkin Duniya. Reuters
Talla

An dai kama likitan ne sakamakon korafin da wata mara lafiya tayi bayan likitan Noel Kekere ya mata aiki. 

A ranar 21 ga watan Satumbar 2021, rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da safarar sassan jikin mutum.

Haka zalika, a watan Maris din 2023 ne, kotu a Birtaniya ta tabbatar da samun tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, da matarsa, Beatrice, da laifin safarar sassan jikin mutum.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton Tasi'u Zakari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.