Isa ga babban shafi

Cutar kyandar biri ta kashe mutane a Spain da Brazil, karon farko a wajen Afirka

Spain da Brazil sun sanar da mutuwar farko da suka samu masu nasaba cutar ƙyandar biri, yayin da Spain din ta sake samun karin mutun daya da ya mutu a wannan Asabar, wanda ke zama mutuwar farko dake da nasaba da cutar a wajen Afirka.

Wata mata tana ƙe da kwalbar "alurar rigakafin ƙwayar cutar kyandar biri" 25 ga Mayu, 2022.
Wata mata tana ƙe da kwalbar "alurar rigakafin ƙwayar cutar kyandar biri" 25 ga Mayu, 2022. REUTERS - DADO RUVIC
Talla

Spain na daya daga cikin kasashen da cutar ta fi kamari a duniya, inda mutane 4,298  suka harbu da ita, a cewar cibiyar kula da cututtuka masu saurin yaduwa ta kasar.

"Daga cikin marasa lafiya 3,750 ... 120 na kwance a asibiti sannan biyu sun mutu," in ji ma'aikatar lafiya ta Spain a cikin wani rahoto.

Brazil

A Brazil, wani mutum dan shekara 41 ya mutu sakamakon kamuwa da cutar kyandar biri, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar a ranar Juma'a.

Mutumin, wanda kafafen yada labaran kasar suka ce yana da matsalolin garkuwar jiki, ya mutu ranar Alhamis a Belo Horizonte, babban birnin jihar Minas Gerais da ke kudu maso gabashin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.