Isa ga babban shafi

Mutane dubu 17 sun harbu da cutar kyandar biri a kasashe 74 - WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cutar kyandar biri ko kuma ‘monkeypox’ a matsayin babbar barazana ga kasashen duniya ganin yadda zuwa yanzu cutar ta harbi mutane kusan 17,000 a kasashe 74.

Sakatare Janar na hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Sakatare Janar na hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus. AP - Salvatore Di Nolfi
Talla

Shugaban Hukumar Tedros Gebreyesus ya sanar da haka yau, yayin ganawa da manema labarai, inda ya ke cewa halin da cutar ta kyandar biri ke ciki a wannan lokaci ya zama babbar barazana ga duniya.

Gebreyesus ya ce kwamitin kwararrunsa da ya gudanar da taro a ranar alhamis ya kasa cimma matsaya akai, saboda haka nauyi ya rataya akan sa domin yanke hukunci da kuma ankarar da duniya.

Matsayin Hukumar shi ne hadarin cutar ya na matakin da za a iya bayyana shi a matsayin matsakaici a shiyoyi 5 da ke duniya amma kuma banda yankin Turai wanda matsalar ke da girma.

Alkaluman Hukumar yaki da Cututtukan Amurka sun bayyana cewar cutar ta kama mutane sama da dubu 16 da 800 a kasashe 74 ya zuwa jiya juma’a, kuma an samu karuwar masu harbuwa da cutar a Yammaci da Tsakiyar Afirka tun daga farkon watan Yuli.

Hukumar tace kasha 98 na wadanda suka harbu da cutar ’yan luwadi ne da kuma masu neman maza da mata a lokaci guda.

Gebreyesus ya bukaci kasashen duniya da suyi aiki tare da al’ummomin dake neman maza domin samar da bayanan da zasu kare su daga harbuwa da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.