Isa ga babban shafi

Sama da mutane dubu 6 suka harbu da kyandar biri a duniya - WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta baiyana cewar mutane sama da dubu 6 ne suka kamu da cutar kyandar biri daga kasashe 58 a fadin duniya.

Gwajin cutar kyandar biri
Gwajin cutar kyandar biri REUTERS - DADO RUVIC
Talla

Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce za su sake shirya wani taro da zai ba da shawara kan ayyana barkewar cutar a matsayin abinda ke bukatar kulawar gaggawa.

A taron da suka gudanar a ranar 27 ga watan Yuni, kwamitin ya yanke shawarar cewa barkewar cutar, bai kai a ayyana ta ba a matsayin annoba ba, duk kuma da karuwar yaduwar cutar a kasashen Afirka.

Turai

Tedros ya ce kusan kashi 80% na bullar cutar, an same tane a Kasashen Turai.

Cutar ta kyandar Biri da ta fara yaduwa a farkon watan Mayun da ya gabata, na da alamun mura da kuraje da dai sauran su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.