Isa ga babban shafi
AFIRKA - CUTAR KYANDA

Cutar Kyanda na ci gaba da addabar kasashen Afirka

An samu karuwar cutar Kyanda da kashi 400 a kasashen Afrika sakamakon jinkirin yi wa kananan yara riga-kafin cutar kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana.

Wani yaro da ke karbar rigakafin cutar kyanda
Wani yaro da ke karbar rigakafin cutar kyanda Reuters
Talla

Kashi 20 na kasashen Afirka sun ba da rahotannin bullar cutar kyanda a rubu'in farko na wannan shekara da muke ciki, wanda ya kasance fiye da yadda ta bulla a shekarar 2021. Yankin na Afirka ya samu barkewar wannan mummunar cutar har kusan dubu 17,500 a tsakanin watannin Janairu da Maris

Hukumar lafiyar ta Duniya da ta asusun tallafa wa kananan Yara na majalisar dinkin duniya UNICEF sun ba da sanarwa a majalisar, cewa yanayin tasirin cutar a wannan shekara yakai kashi 80 a fadin duniyar.Tare da gargadin cewar hakan na iya haifar da barkewar wasu cutukan in har ba yi musu diban karen mahaukaciya ba

Dama dai Mafi akasari batun barkewar cutar ta kyanda tafi karfi a Nahiyar Afirka. Yayin da Ofishin hukumar ta lafiya WHO a Afirka ya kara da cewar barkewar wasu cututtukan da akan iya rigakafin su ma sun zama ruwan dare a nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.