Isa ga babban shafi

Tarayyar Turai ta amince da sabon rigakafin cutar kyandar biri

Hukumar Tarayyar Turai ta amince da maganin cutar kyanda don magance kyandar biri, bayan hukumar lafiya ta duniya ta ayyana cutar ta biri a matsayin barazana ga harkokin kiwon lafiya a duniya.

Alamun gwajin cutar kyandar biri kenan da ke nuna wasu na dauke da ita, inda wasu kuma basa dauke da ita.
Alamun gwajin cutar kyandar biri kenan da ke nuna wasu na dauke da ita, inda wasu kuma basa dauke da ita. REUTERS - DADO RUVIC
Talla

Wannan na zuwa ne bayan da WHO ta fitar da rahoton cewa kusan mutum 16,000 ne suka harbu da cutar daga cikin kasashe 72.

Hukumar Tarayyar Turai ta tsawaita ba da izinin tallata rigakafin cutar na kamfanin, Imvanex, don samar da kariya daga cutar kyandar biri bisa ga shawarar da hukumar kula da magunguna ta EU ta bayar.

Bullar cutar

Tun a shekarar 2013 ne dai kungiyar tarayyar Turai ta amince da maganin cutar kyanda na kamfanin Imvanex.

Masana kiwon lafiya sun yi la'akari da yiwuwar amfani da rigakafin cutar ne saboda kamanceceniya tsakanin kwayar cutar da ta kyandar biri.

Amma kuma bincike ya nuna cewa kyandar biri bata da hadari ko kuma saurin yaduwa kamar kwayar cutar kyanda, wadda aka samu nasarar kawar da ita a shekarar 1980.

An dai samu karuwar masu kamuwa da cutar kyandar biri tun a farkon watan Mayu musamman a kasashen Yamma da tsakiyar Afirka wato inda cutar ta dade tana yaduwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.