Isa ga babban shafi

Kotun Faransa ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga maharin birnin Paris

Kotu a Faransa, ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga mutum daya tilo da ya rage cikin maharan birnin Paris na shekarar 2015, harin da ya hallaka mutane 130 baya ga jikkata wasu da dama.

Zaman shari'ar karshe ga Maharin birnin Paris Salah Abdeslam.
Zaman shari'ar karshe ga Maharin birnin Paris Salah Abdeslam. AP - Christophe Ena
Talla

Maharin Salah Abdelsalam mai shekaru 32 dan asalin kasar Morocco da ke da shaidar zama a Belgium, jami’an ‘yan sanda sun kame shi ne watanni 4 bayan harin gabanin mika shi ga mahukuntan kasar don gurfanar da shi gaban kotu tare da yi masa hukunci kan hannu a harin mafi muni a tarihin Faransa.

Zaman shari’ar na yau laraba karkashin jagorancin manyan alkalai 5, babban alkalin zaman ya umarci daure Salah na tsawon rayuwarsa a gidan yari baya ga hukuncin ga sauran mutane 19 da ke hannu a farmakin wadanda galibi ke da hukuncin da ya fara daga shekaru 2 zuwa daurin rai da rai.

Ilahirin maharan na birnin Paris ko dai an kashe su nan ta ke ko kuma su tashi kansu da bama-bamai a yayin farmakin na watan Nuwamban 2015, sai dai duk da hakan zaman kotun ya yanke musu hukuncin.

Daruruwan wadanda suka tsira daga harin ne suka halarci zaman kotun na karshe a yau laraba, bayan faro shari’ar a watan Satumban bara.

Zaman Kotu

Tun bayan faro shari’ar cikin watan Satumban 2021 Salah Abdelsalam ya bayyana kansa a matsayin mayakin IS yayinda ya ki bayar da hadin kai sai dai a zaman nay au, anga yadda ya karaya tare da neman yafiyar jama’a da kuma sassauci daga alkalai.

Lauyoyin da ke kare Salah, sun bukaci kotu ta yi sassauci ga hukuncin na daurin rai da rai da suka bayyana a matsayin wanda ya yi tsauri matuka.

Salah Abdeslam na iya samun sassauci daga kotu musamman la’akari da dokar afuwa da Faransa ke amfani da ita duk da cewa tun daga 1994 zuwa yanzu sau 4 kacal aka taba amfani da ita a aikace.

Bayanin Salah Abdeslam

A jawabinsa gaban alkali yayin zaman shari’ar Salah ya bayyana cewa bayan karbar aikin kaddamar da farmakin, ya sauya tunani dalilin da ya sanya shi cire damarar bom din da ke jikinsa tare da guduwa kauyensu inda dandazon ‘yan ta’adda ke tattare a Belgium.

Harin 2015

Cikin watan Nuwamban 2015 ne tawagar maharan 10 suka shiga birnin Paris tare da tayar da bama bamai a gidajen shakatawa, filin wasa da wajen kade-kade da kuma mashayu wanda ya hallaka mutane 130 baya jikkata wasu gommai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.