Isa ga babban shafi
Faransa - Ta'addanci

Wanda ake zargi da kai harin Paris ya nemi afuwa

Mutun daya da ya tsira da rayuwarsa daga cikin ‘yan ta’addan da suka kai hari a watan nuwambar shekarar 2015 a birnin Paris Salah Abdeslam, ya nemi afuwar mutanen da suka hallaka a wannan hari.

Harabar kotun Faransa da ake shari'ar wadanda suka kai harin 13 ga watan Nuwambar 2015.
Harabar kotun Faransa da ake shari'ar wadanda suka kai harin 13 ga watan Nuwambar 2015. AFP - ALAIN JOCARD
Talla

Abdeslam ya nemi wannan afuwa ne a wannan Juma’a, lokacin da yake amsa tambayoyi daga alkalan da ke yi masa shari’a dangane da wannan hari da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 130.

Abdeslam, ya ce ya yi nadama a game da wannan lamari, saboda haka yana neman afuwar ‘yan uwa da kuma aminan wadanda suka hallaka a wannan hari, kuma ya nemi afuwar ne a daidai lokacin da yake zubar da kwallo.

Wannan Jumma’a ita ce rana ta uku kuma ta karshe a shaidar da wannan dan ta’adda ke gabatar wa alkalan da ke guganar da wannan shari’a, kuma a matsayinsa na mutum daya da ya tsira da rayuwarsa bayan kashe sauran abokan tafiyarsa.

Harin Bataclan

A ranar 13 ga watan nuwambar shekara ta 2013 ne, suka kai hare-hare a wurare da dama da ke birnin Paris, da suka hada da gidan rawa da Bataclan, da filin wasan kwallon wanda a lokacinsa akwai tsohon shugaban kasar Francoiis Hollande zaune a cikin ‘yan kallo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.