Isa ga babban shafi
Faransa-ta'addanci

Kotun Faransa ta fara karbar shaidar wadanda suka tsira a harin 2015

Wadanda suka tsira daga hare-haren ta’addancin birnin Paris na watan Nuwamban shekarar 2015 sun fara ba da shaida a wata shari’a da aka fara a yau Talata, inda aka gurfanar da mutane fiye da 10 da ake tuhumar su da aikata ta’addancin.

Zaman sauraron shari'ar maharin birnin Paris.
Zaman sauraron shari'ar maharin birnin Paris. AP - Thibault Camus
Talla

Daya bayan daya ne dai za a rika karbar shaida cikin makwanni masu zuwa, daga mutane 300 da suka tsira daga hare-haren ta’addancin da kuma dangin wadanda aka kashe a ranar 13 ga watan Nuwamba, fiye da shekaru 5 ada suka gabata.

Hare -haren kunar bakin wake da kuma harbin kan mai uwa da wabi da bindigogi da wasu gungun mahara kashi uku suka kai kan mashaya, gidajen cin abinci da zauren kide-kide na Bataclan da filin wasa da ke birnin Paris wadanda daga baya kungiyar IS ta dauki alhaki ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 130 yayin da kusan 350 suka jikkata.

Cikin watan nan ne Kotun kasar da ke birnin Paris ta fara sauraron shari'ar mutum guda da ya tsira da ransa cikin maharan da suka kaddamar da farmakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.