Isa ga babban shafi

Kotu a Faransa ta fara shari'a kan maharan birnin Paris na 2015

Faransa ta fara shari’ar maharan 2015 su 20 yau laraba, shari’ar da ke matsayin mafi girma da kasar ke gani kan harin na watan nuwamba da ya hallaka mutane 130, inda bayanai ke cewa za a kwashe watanni 9 ana gudanar da shari’ar gabanin zartas da hukunci.

Mahalarta kotun da ke sauraron karar Salah Abdeslam maharin birnin Paris na watan Nuwamban 2015.
Mahalarta kotun da ke sauraron karar Salah Abdeslam maharin birnin Paris na watan Nuwamban 2015. REUTERS - GONZALO FUENTES
Talla

Mutane 14 da ake zargi da kaddamar da farmakin ciki har da guda cikin maharin da aka kama a raye sun hallara a kotun ta birnin Paris yayinda sauran 6 za a gudanar da shari’ar ba tare da halartarsu ba.

Harin na ranar 13 ga watan Nuwamban 2015 da mutanen 20 suka kaddamar kan gidajen barasa da na abinci da kuma gidan rawa shi ne mafi muni da Faransa ta taba gani, da ya hallaka mutane 130 baya ga jikkata gommai.

Shari’ar wadda aka warewa kwanaki 145 za ta bai wa lauyoyi 330 damar sanya baki baya ga wadanda harin ya shafa 300 da za su bayyana gaban kotu yayinda shi kansa tsohon shugaban kasar da harin ya faru a lokacin mulkinsa Francois Hollande zai yi jawabi gaban kotun.

Salah Abdeslam mai shekaru 31 a yanzu, haifaffen kasar Belgium amma ya ke dauke da shaidar zama dan kasa ta Morocco da Faransa shi ne mahari da ya tilo da aka kama da ransa bayan da ya yadda damarar bom dinsa a wajen harin gabanin kama shi a Brussels cikin shekarar 2018, da aka bashi damar magana gaban kotun yau bayan fara shari’a ya fara da cewa ‘‘Ya shaida babu abin bautawa bisa gaskiya da cancanta sai Allah kuma Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wasallam shi ne manzon tsira’’.

Abdeslam wanda ke da taurin kan magana gaban mahukunta tun bayan kama shi, ya ce ya ajje kowanne aiki don fara jihadi da kungiyar IS.

Guda cikin wadanda suka tsira daga harin na 2015, Arthur Denouveaux kuma yanzu ya ke jagorancin kungiyar tabbatar da adalci ga wadanda harin ya shafa ya ce suna ganin shari’ar za ta dauki lokaci har zuwa nan da watan Mayun 2022.

Matukar dai dukkanin wadanda ake tuhuma da kaddamar da harin suka amsa laifinsu kai tsaye kotun za ta zartas musu da hukuncin kisa ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.