Isa ga babban shafi

An bukaci hukuncin rai da rai kan mutumin da ya kai harin Paris na 2015

Masu gabatar da karar Faransa kan shari'ar harin da aka kai birnin Paris sun bukaci da a yanke hukuncin daurin rai da rai ba tare da neman afuwa ba ga babban wanda ake zargi da kai harin watan Nuwamban 2015 wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 130 a harin ta'addanci mafi muni da Faransa ta gani.

Salah Abdeslam dan kasar Faransa mai shekaru 32 da haihuwa, shi ne kadai maharin da ya tsira da rayuwarsa daga cikin maharan da suka bude wuta a dakin kide-kide na Bataclan da kuma gidan shan shaye, tare da tayar da bama-bamai a filin wasanni na Stade de France.
Salah Abdeslam dan kasar Faransa mai shekaru 32 da haihuwa, shi ne kadai maharin da ya tsira da rayuwarsa daga cikin maharan da suka bude wuta a dakin kide-kide na Bataclan da kuma gidan shan shaye, tare da tayar da bama-bamai a filin wasanni na Stade de France. REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Salah Abdeslam dan kasar Faransa mai shekaru 32 da haihuwa, shi ne kadai maharin da ya tsira da rayuwarsa daga cikin maharan da suka bude wuta a dakin kide-kide na Bataclan da kuma gidan shan shaye, tare da tayar da bama-bamai a filin wasanni na Stade de France.

Bukatar cewa kada Abdeslam ya samu yuwuwar yin afuwa abu ne mai wuya a Faransa, inda ake sakin fursunonin da ke zaman daurin rai da rai bayan shekaru 20 zuwa 25.

Har ila yau, ana tuhumar wasu mutane 19 da ake zargi da wasu laifuka daban-daban na taimakawa maharan, kama daga bayar da tallafin kayan aiki zuwa shirya hare-haren ko kuma samar da makamai.

Masu gabatar da kara sun kuma bukaci a yanke musu hukuncin daurin rai da rai ga wadanda ake zargin 'yan kungiyar IS ne, Osama Krayem dan kasar Sweden da kuma dan Tunisiya Sofien Atari, da kuma shekara daya ga Mohamed Abrini, dan kasar Belgium da ake zargi da bayar da makamai da kayan aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.