Isa ga babban shafi
Faransa-ta'addanci

Ban kashe kowa ba a farmakin da na kai- Maharin Paris

Mutum daya tilo da ya rage da rai, cikin wadanda suka kaddamar da harin ta’addancin birnin Paris na shekarar 2015 ya dage kan cewa ba shi da hannu a kisan ko da mutum guda cikin mutanen da suka rasa rayukan su.

Zaman shari'ar Salah Abdeslam.
Zaman shari'ar Salah Abdeslam. AFP - BENOIT PEYRUCQ
Talla

Wannan dai shi ne karon farko da Salah Abdlesalam mai shekaru 32 ya sauya matsayar sa na cewa bashi da hannu a harin da ya hallaka mutane sama da 130.

A cewar sa bai zama sanadin ko da kwarzane a jikin wani ba, a don haka yana bukatar kotun ta wanke shi ba tare da bata lokaci ba, a wani sabon al’amari da ya zowa kotun a bazata, la’akari da yadda ya sha amsa laifukan sa a baya.

To amma Abdelsalam ya jadadda kasancewar sa mamba a kungiyar IS to sai dai ya soki matakin kotun na shirin yanke masa hukuncin kisa, saboda laifin.

Haka kuma Abdelslam ya nesanta kansa da wadanda suka kaddamar da harin a wannan lokaci, yana mai cewa da fari da shi aka shirya kai harin amma lokacin da ake gab da kai harin ne ya sauya ra’ayin sa.

Dama dai tun 2016 da aka kama Abdelsalam a kasar Belijum, bayan shafe watanni ana bincike, ya yi kememe wajen amsa tambayoyin masu bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.