Isa ga babban shafi

Macron ya yi watsi da yunkurin kafa gwamnatin hadin gwiwa a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gabatar da jawabin farko tun bayan zaben ‘yan majalisar dokokin da aka gudanar ranar lahadin da ta gabata, inda ya ce ‘yan adawa sun ba shi tabbacin cewa za su yi aiki da shi domin kare muhimman batutuwan da suka shafi kasar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

A jawabin da yayi da yammacin ranar Laraba, shugaba Macron ya bayyana yadda ya shafe tsawon yini biyu yana tattaunawa da shugabannin jam’iyyu daban daban dake da tasiri a sabuwar majalisar dokokin Faransa, wadanda ya ce sun tabbatar cewa ba za su kawo cikas ga cigaban kasarsu ba.

Sai dai a jawabin da ya yiwa jama’ar kasar daren Larabar da ta gabata, Macron yayi watsi da duk wani yunkuri na kafa gwamnatin hadin kai a kasar, inda ya bukaci ya bukaci bangarorin siyasar kasar da su bada hadin kai wajen kawo karshen tsaikon da aka samu na kulla yarjejeniyar kafa sabuwar gwamnati.

Zaben da aka yi a karshen mako ya nuna cewar Macron ya gaza samun Karin kujeru 44 da yake bukata domin samun rinjaye a majalisar dokoki, abinda zai bashi damar kafa gwamnati ba tare da kulla kawance ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.