Isa ga babban shafi

Zaben Faransa : Macron na neman rinjaye a majalisun dokokin kasar

Yau Faransawa ke kada kuri'a a zagayen farko na zaben 'yan majalisar dokokin kasar inda shugaba Emmanuel Macron ke fatan samun rinjayen don samun goyon bayan shirinsa na garambawul yayin da masu ra'ayin mazan jiya da wasu jam’iyyun adawa da suka kula kawance ke neman kawo cikas ga burinsa.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yayin kada kuri'a a zaben majalisun dokoki. 12/06/22.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yayin kada kuri'a a zaben majalisun dokoki. 12/06/22. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Zaben 'yan majalisar dokokin kasar mai kujeru 577 nada tsarin zagaye na biyu, kuma baza’ayi sanin sabuwar majalisar ba har sai bayan zagaye na biyu na zaben a ranar 19 ga watan Yuni.

Macron na kokarin samun rinjaye wajen aiwatar sabbin alkawura da ya dauka na sauyi a gwamnatinsa, bayan cikas da ya samu a gwamnatin sa na farko da zanga-zangar masu riguna dorowa da annobar korona da kuma yakin Ukraine suka mamaye.

Sama da Faransawa milyan 43 ne suka karbi katunan zabe  domin sabunta wannan majalisa mai dauke da 'yan majalisu 577 inda ake da 'yan takara sama da dubu 6.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.