Isa ga babban shafi

Faransawa na kada kuri'a a zaben shugabancin kasarsu zagaye na 2

An bude rumfunan zabe a kasar Faransa, domin kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa tsakanin shugaba mai ci Emmanuel Macron da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen mai tsatsauran ra'ayi.

Wata mata yayin daukar. takardar kada kuri'a akan teburi, yayin zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Faransa, a birnin Lyon, 24 ga Afrilu, 2022.
Wata mata yayin daukar. takardar kada kuri'a akan teburi, yayin zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Faransa, a birnin Lyon, 24 ga Afrilu, 2022. REUTERS - STEPHANE MAHE
Talla

Ana sa fara bayyana sakamakon zaben da misalin karfe 8:00 na dare, karfe 6 kenan agogon GMT.

Macron dai ya shiga zaben ne tare da hasashen sakamakon wasu kuri’un jin ra’ayin jama’a da suka nuna cewar shi ake kyautata zaton zai lashe zaben na ranar Lahadi, bayan lashe na zagayen farko da ya yi a ranar 10 ga watan nan na Afrilu, da kashi 28 na kuri’un da aka kada, yayin da Le Pen ke da kashi 23.

Sai dai manazarta sun gargadi shugaban mai ci wanda ya hau karagar mulki a shekara ta 2017 yana da shekaru 39 da cewar, ka da ya dauka alkaluman ra’ayoyin jama’ar da kuma hasashen masana za su ishe shi samun nasarar da yake nema, domin kuwa reshe ka iya juyewa da mujiya idan har adadin kusan kashi 10 na wadanda basu yanke shawarar wa za su zaba ba, suka karkata ga bangaren ‘yan adawa.

Faransawa miliyan 48 da akalla dubu 700 ne suka cancanci kada kuri'a a zaben shugabancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.